Kalli Hotunan Mijin Aisha Tsamiya

Daga Hotunan auren Aisha Tsamiya, zuwa lambar wayar Aisha Tsamiya, da dai sauran bincike, ya nuna irin dimbin soyayyar da mutane ke yiwa Aisha da kokarinsu na sanin yadda bikin nata ya kasance da yadda ake tuntubar juna tare da mika mata sakon taya murna.

Aisha Tsamiya tayi aure amma mutane da yawa suna son sanin wanene Mijinta. Hotunan nasa suna son mutane da yawa.

Sunan mijinta Alhaji Abubakar Buba. An ga hotonsa a shafin daya daga cikin aminiyar jarumar wato shafin Umma Shehu inda ta saka hoton a cikin labarinta. Za mu iya cewa wannan sanarwa ta 2022 ta zo da sabon salo, musamman a nan masana’antar KannyWood, inda daga shiga sabuwar shekara zuwa manyan jarumai uku. Mata biyu wato (Aisha Tsamiya da Hafsat Idris) da namiji daya wato (Ali Muhammad, Ali Artwork). Muna fatan Allah ya basu hadin kai da kwanciyar hankali a gidan aurensu